Labaran zubar da ciki da ba a bayyana ba daga Najeriya.
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki haramun ne a Najeriya, amma bai hana dubban mata aikata shi ba. Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin haɗari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo ƙarshen ciki. A cikin wannan jerin labaran, Hannah, marubuciya, ƴar jarida kuma jakadiyar labarai na CotW ta yi magana da mata waɗanda duk da haɗari sun yanke shawarar zubar da ciki.
Nigeria, Western Africa
Story by H.T. Jagiri. Edited by Veronica Burgstaller. Translated by Zainab Alhassan
Published on August 18, 2022.
This story is also available in
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na nuna wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki ya saɓawa doka a Najeriya, amma bai hana dubban mata aikata shi ba.Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin hatsari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo karshen ciki.A matsayi na na mai son kare ƴan'cin mata da daidaiton jinsi, na so ne in binciko tasirin aikata laifin zubar da ciki a Najeriya.Saboda haka na nemi matan da suka yi kasada da rayukan su don su kawo ƙarshen ciki.Wannan shi ne labarin Seyi*.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a na shekarar 2017. Titin ya cika da ƙayatarwa yayin da al’ummar Tanke Ilorin[1] ke gudanar da harkokin su na yau da kullum, sanye da kaya masu ƙayatarwa. Hijabai da Abayas[2] na kaloli da salo daban-daban sun ƙawata tituna kamar yadda ake bikin Idin Babbar Sallah[3]. Seyi tana ɗaya daga cikin taron jama'an da suke kan titi. Tana kan hanyar ta ne ta domin ta sayo magungunan da za su zubar mata da ɗan ƙaramin a cikin da yake girma jikin ta. Makonni kaɗan da suka wuce, ta gano tana dauke da yaro a cikin ta. duka-duka shekarun ta sha-bakwai ne, kuma tana shekarar ta biyu a Jami'ar Ilorin, ta san ba za ta iya kula da yaron ba saboda ba ta shirya zama uwa a yanzu ba.
Na ji kamar duniya ta ta rushe lokacin da na sami sakamakon gwajin. Na gaya wa saurayi na, sai ya ce ba za mu iya riƙe shi ba. ba sai ya gamsar da ni ba. Na san ba zan iya riƙe yaro ba. Har yanzu ni yarinya ce da kai na. Nan da nan bayan na yi zaɓi, na shiga yanar gizo don neman mafita. Ta hakane har na ilimantu game da Mifepristone da Misoprostol." Ta yi murmushin bacin rai da laɓɓanta yayin da take magana.
Titin ya cika da rayuwa yayin da ƴan kasuwa ke baje kolin kayan su ga duk wanda ya wuce, suna kiran hankalin su da murya mai sauti. shagon magani na farko da Seyi ta je ta samu mai shagon sanye da hijabi[4].
Na isa kantin magani na farko, sai na haɗu da wata ƴar uwa sanye da hijabi. Na gaya mata ina so in samu Mifepristone da Misoprostol. Nan take fuskar ta ya canza, ta fara magana da ƙarfi yadda kowa zai ji cewar ba ta sayar da magungunan zubar da ciki. Na ɗauka karshen kenan. Na bar kantin maganin a kunyace. Amma na san komawa gida ba tare da magungunan ba ba zaɓi ba ne. Na san ajiye cikin nan baya cikin tunani na. Don haka na yanke shawarar gwada wani kantin magani. kantin magani na gaba ba wani babba ba ne, kuma mai kantin magani mai ciki zai yi wuya ta siyar da maganin zubar da ciki. Ta bada bayan wani lokaci. Da na ga mai sayar da magunguna na da ciki, sai na kusa yin dariya da ƙarfi. Na ji kaman Allah ne ya azabtar da ni. Na ji kamar na zama abin ban dariya ga Allah da mala'iku''
Ba zan iya kiran kowa ba saboda na san illar hakan. Haka na kwanta a ƙasa ina jiran mutuwa ta zo.
Seyi ta isa hostel ɗin ta. Wani ɗaki mai ɗaki wanda kusan babu kowa a ciki, sai katifa da tarin littafai a ƙasa. Kayan tufafin yana gefen hagu na ɗakin, shekaru da yawa da aka yi ana amfani da su sun riga sun sa sassan katakon durowan ya firfita. Seyi tayi amfani da magungunan nan take bayan ta isa ɗakin ta. Sai da ta jira ta ga ko zai fara aiki, bayan awa ɗaya bai yi ba, sai ta ƙara biyu. Ba'a jima ba sai ta fara zubar da jini sosai, tare da tsananin ciwon mara.
Ji nake kamar wani abu ya matse ciki na, ciwo ne ba na jurewa ba, kuma duk minti ɗaya sai na ji kai na kaman zan wuce da gaggawa. Na yi tunanin zan mutu. Ba zan iya kiran kowa ba saboda na san illar hakan.
Sai na kwanta a ƙasa, ina jiran mutuwa ta zo"
Ta yi sa'a, hakan bai faru ba.
*An canza sunaye masu alamar alama don kare asalin waɗanda suka zanta da wakilan World on condition of anonymity.
[1] Tanke birni ne, a cikin al'ummar IIorin, babban birnin jihar Kwara a Najeriya.
[2] Abaya Tufafi ne wanda ba shi da nauyi da
[3] lokacin biki ne ga musulmai.
[4] mace musulma tana sanya hijabi, A Najeriya ba duk mata musulmai ne ke sanya hijabi ba.
Karanta Kashi Na Biyu - Labarin Amina na wannan shiri mai suna Labaran Zubar da Ciki da Ba a Bayyana ba daga Najeriya a nan.
How does this story make you feel?
Follow-up
Do you have any questions after reading this story? Do you want to follow-up on what you've just read? Get in touch with our team to learn more! Send an email to [email protected].
Talk about this Story
Please enable cookies to view the comments powered by Disqus.
Subscribe to our Monthly Newsletter
Stay up to date with new stories on Correspondents of the World by subscribing to our monthly newsletter:
Other Stories in Hausa
Tags
Explore other Topics
Get involved
At Correspondents of the World, we want to contribute to a better understanding of one another in a world that seems to get smaller by the day - but somehow neglects to bring people closer together as well. We think that one of the most frequent reasons for misunderstanding and unnecessarily heated debates is that we don't really understand how each of us is affected differently by global issues.
Our aim is to change that with every personal story we share.
Community Worldwide
Correspondents of the World is not just this website, but also a great community of people from all over the world. While face-to-face meetings are difficult at the moment, our Facebook Community Group is THE place to be to meet other people invested in Correspondents of the World. We are currently running a series of online-tea talks to get to know each other better.