Labaran Zubar da Ciki da Ba a Bayyana ba daga Najeriya
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki haramun ne a Najeriya, amma bai hana dubban mata aikata shi ba. Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin haɗari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo ƙarshen ciki. A cikin wannan jerin labaran, Hannah, marubuciya, ƴar jarida kuma jakadiyar labarai na CotW ta yi magana da mata waɗanda duk da haɗari sun yanke shawarar zubar da ciki.
Nigeria, Western Africa
Story by H.T. Jagiri. Translated by Zainab Alhassan
Published on September 8, 2022.
This story is also available in
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki haramun ne a Najeriya, amma hakan bai hana dubban mata aikata shi ba. Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin haɗari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo ƙarshen ciki. A matsayi na na wanda ke son kare ƴan'cin mata da daidaiton jinsi, na so in binciko illar laifin zubar da ciki a Najeriya. Don haka na nemo matan da suka sadaukar da rayukan su don su kawo ƙarshen ciki. Wannan shi ne labarin Amina* wata yarinya ƴar shekara sha-uku da wani abokin ɗan'uwan ta ya mata fyaɗe, ta shiga wani yanayi mai wani ban tausayi. Ina kallon ta tana magana tana rawar jiki tana matse yatsun hannun ta sosai. Mutum zai yi tunanin iska ta yi sanyi, amma na fi ta sani.
"Na je wurin wani aboki na da yamma wata rana, sai ya ba ni giyan kwakwa [1] a lokacin da muke wasan ludo[2]. na gaji sosai sa, na garzaya gida, da na mike zan tafi, sai na nayi bacci na ɗan wani lokaci, lokacin da na tashi maraice ta yi sosai, da sauri na tashi na nufi gida, lokacin da na tashi zan tafi, sai na ji wani irin zafi a cikin farji na da cinya ta, amma sai na gama cewa “Ibotan” ne (ciwon cinya) ashe ba haka bane na yi kuskure.
Na isa gida, amma ban iya tuna komai daga abin da ya faru a wurin aboki na ba. Bayan ƴan watanni na gano ina da ciki. Na ruɗe, domin a iya sani na ban taɓa yin jima'i ba. duka-duka shekara na sha-uku ne. Lokacin da iyaye na suke yi mini tambayoyi, sai na soma tuno wasu abubuwa. Na je na fuskanci aboki na, sai ya ce shi ne ya yi min fyaɗe. Na gaya wa iyaye na, gaba-ɗaya muka je mu gana da iyayen sa. Ya musanta komai. Mahaifin sa ya kira ni ƴar iska ya ce wa iyaye na ina buɗe ƙafafuna ga duk wanda ya zo sa mota. zuciya ta ta karaya. Na roƙe shi ya faɗi gaskiya, amma ya kau da kai daga gare ni. Ni da iyaye na muka bar gidan cike da kunya. Iyaye na suka tsani ni saboda abin kunyan da na kawowa dangi. Babu wanda ya ya yarda da ni. Don haka suka yanke shawarar ba zan haifi yaron ba. Mahaifiya ta ta kai ni wajen likita, sai ya ce An yi lattin zubar da ciki. Saboda ba ta son ta yi rainon ɗan wani, ta ɗauke ni ta kai ni wajen wani likita wanda ya yarda.
“Asibitin” gidan wani matashin likita ne, wanda ya yi amfani da ɗaya daga cikin ɗakunan da ke ɗakin sa mai ɗaki uku a matsayin asibitin zubar da ciki. An yi wa bangon ɗakin fentin fari, kuma akwai taɓo wanda zaka yi zaton wani abu a wasu sassan bangon. An yi amfani da wani ƙaton kyalle mai kauri an rufe taga wanda ya sa ɗakin yayi duhu. Ga waɗanda ba su taɓa shiga ba, ɗaki ne kawai. Ana iya ganin fitilar da ba ta da kyau a kan abin da ke kama da tebur, kuma ana iya ganin siffar gadon asibiti.
Ni ma ba a ba ni daman na yi ihu ba don babu wanda ya san me ke faruwa, na cije leɓe na har sai da suka yi jini na riƙe bakin gadon.
Ya ce in kwanta in baje ƙafafuna a buɗe. Na kasa tantance abin da ya saka a ciki na, amma na ji ƙarfe ya taɓa fata ta. Na ji zafi mai zafi yayin da yake gogewa yana tsotsa. Ni ba a ba ni daman ihu ba don babu wanda ya san me ke faruwa, sai na cije leɓena har sai da suka yi jini na riƙe bakin gadon. Bayan ya gama sai ya ba ni sachet na paracetamol ya mayar da ni gida.”
Ta tsaya ta saki hawayen da take riƙe tun da ta fara magana. Na ɗan huta na awa ɗaya, don in ba ta lokaci ta huta sannan na nima na samu na huta bayan na saurari maganganun ta. Akwai tambaya ta ƙarshe da nake buƙatar yi mata. Shin tayi nadamar zubar da cikin.
"Kamar yadda abin yake da ban tausayi da muni, da na haifa masa yaro zai fi muni. A gaskiya na kasa tantance yadda rayuwa ta za ta kasance a yanzu idan na haifi yaron."
[1] Kwakwa abin sha ne na giyar da ake yi da ruwan kwakwa.
[2] Ludo wasa ne da ake yin shi.
*An canza sunaye masu alamar tauraro don kare sunayen waɗanda suka yi magana da Correspondents of the World bisa sharaɗin sakaye sunayen su.
Read Part 3 - The Doctor's View of this story series on Untold Abortion Stories from Nigeria here.
How does this story make you feel?
Follow-up
Do you have any questions after reading this story? Do you want to follow-up on what you've just read? Get in touch with our team to learn more! Send an email to [email protected].
Talk about this Story
Please enable cookies to view the comments powered by Disqus.
Subscribe to our Monthly Newsletter
Stay up to date with new stories on Correspondents of the World by subscribing to our monthly newsletter:
Other Stories in Hausa
Explore other Topics
Get involved
At Correspondents of the World, we want to contribute to a better understanding of one another in a world that seems to get smaller by the day - but somehow neglects to bring people closer together as well. We think that one of the most frequent reasons for misunderstanding and unnecessarily heated debates is that we don't really understand how each of us is affected differently by global issues.
Our aim is to change that with every personal story we share.
Community Worldwide
Correspondents of the World is not just this website, but also a great community of people from all over the world. While face-to-face meetings are difficult at the moment, our Facebook Community Group is THE place to be to meet other people invested in Correspondents of the World. We are currently running a series of online-tea talks to get to know each other better.