Labaran Zubar da Ciki da Ba a Bayyana ba daga Najeriya: Ra'ayin Likita (3/4)
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki haramun ne a Najeriya, amma bai hana dubban mata aikata shi ba. Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin haɗari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo ƙarshen ciki. A cikin wannan jerin labaran, Hannah, marubuciya, ƴar jarida kuma jakadiyar labarai na CotW ta yi magana da mata waɗanda duk da haɗari sun yanke shawarar zubar da ciki.
Nigeria, Western Africa
Story by H.T. Jagiri. Translated by Zainab Alhassan
Published on September 18, 2022.
This story is also available in
Ina son ƙarin sani game da abin da likitocin da suke yin aikin da kan su suke tunani game da shi. Wannan shi ne abin da Dr Annie*, wata ƙwararriyar likita a wani sanannen asibiti da ke tsakiyar birnin Legas a Najeriya ta ce game da wannan batu.
Dr Annie ta yi imanin cewa tana yin duk abun da ya dace. Ta yi iƙirarin zubar da cikin ne saboda ta yi imani da bawa mutane dama ta biyu. Ta tuno wani lamari da ya maƙale mata.
"An kawo wata yarinya zuwa asibiti domin zubar da cikin bayan an yi mata fyaɗe, ga alama matashiya ce kuma ba ta da ƙarfi. Binciken da aka yi ya nuna cewa ta cika makonni sha-bakwai da yin ciki. Wannan lamari ne mai sarƙaƙiya saboda ƙarama ce. mai yiwuwa ta ji zafi kaɗan zafi idan aka kwatanta da babbar mace, na fara aikin ne ta hanyar dilating ɗin ta, sai da aka ɗau tsawon lokaci kafin a buɗe mahaifar, da zarar ya yi faɗi sosai yadda ake so, sai na sa na'urar wuƙaƙe a cikin ta, ta zabura, Ba a ba ta maganin kwantar da zogi ba saboda ina son ta kasance mai amsawa, bayan an gama aikin, an sanya mata ido yayin da aka sassauƙar da wani ruwa da jini daga cikin farjin ta.
Abin takaici, dole ne in sake yin aikin saboda wasu abubuwa suka maƙale a cikin mahaifar ta. Dole ta sake shiga cikin yanayin zafin. Ya kasance irin wannan mara daɗi ga yarinya. Bayan an yi mata na biyu, ta yi asarar jini mai yawa, har sai da aka sanya ta a cikin ɗakin kulawa mai tsanani har sai da jinin ya lafa. Ta yi fama don dawo da daidaito a hankali da nutsuwan ta. Lamarin ya yi matuƙar wahala ga tunanin matashiyan.
Zama uwa ba wasan yara bane. Ba daidai ba ne a sanya ta cikin damuwa na tunani da tunanin da ke tattare da shi, ba tare da la'akari da kowane irin tallafin iyali ba. Ya kamata a bar yara su zama ƴaƴan, kuma kada a dinga nuna musu tsana da hantara. A matsayin mu na ƙwararrun kan kiwon lafiya da ke ba da irin wannan gudunmawa, ba mu da ra'ayi ko kaɗan don tilastawa iyaye ko matan da suka zo zubar da ciki. Za mu iya tantancewa da bayyana yiwuwar haɗarin da za a iya shiga waɗanda za su ƙayyade idan za a iya aiwatar da shi ko a'a. A ra'ayi na, ina ganin yana da kyai a ba ta dama ta biyu a rayuwa mai inganci."
*An canza sunaye masu alamar tauraro don kare sunayen waɗanda suka yi magana da Correspondents of the World bisa sharaɗin sakaye sunan su.
Read Part 4 - The Legal Reality of this story series on Untold Abortion Stories from Nigeria here.
How does this story make you feel?
Follow-up
Do you have any questions after reading this story? Do you want to follow-up on what you've just read? Get in touch with our team to learn more! Send an email to [email protected].
Talk about this Story
Please enable cookies to view the comments powered by Disqus.
Subscribe to our Monthly Newsletter
Stay up to date with new stories on Correspondents of the World by subscribing to our monthly newsletter:
Other Stories in Hausa
Explore other Topics
Get involved
At Correspondents of the World, we want to contribute to a better understanding of one another in a world that seems to get smaller by the day - but somehow neglects to bring people closer together as well. We think that one of the most frequent reasons for misunderstanding and unnecessarily heated debates is that we don't really understand how each of us is affected differently by global issues.
Our aim is to change that with every personal story we share.
Community Worldwide
Correspondents of the World is not just this website, but also a great community of people from all over the world. While face-to-face meetings are difficult at the moment, our Facebook Community Group is THE place to be to meet other people invested in Correspondents of the World. We are currently running a series of online-tea talks to get to know each other better.