Labaran Zubar da Ciki da Ba a Bayyana ba daga Najeriya: Gaskiyar shari'a (4/4)
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki haramun ne a Najeriya, amma bai hana dubban mata aikata shi ba. Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin haɗari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo ƙarshen ciki. A cikin wannan jerin labaran, Hannah, marubuciya, ƴar jarida kuma jakadiyar labarai na CotW ta yi magana da mata waɗanda duk da haɗari sun yanke shawarar zubar da ciki.
Nigeria, Western Africa
Story by H.T. Jagiri. Translated by Zainab Alhassan
Published on September 29, 2022.
This story is also available in
Laifin zubar da ciki wani nau'i ne na wariya ga mata. Har yanzu zubar da ciki haramun ne a Najeriya, amma hakan bai hana dubban mata aikata shi ba. Waɗannan matan suna jefa rayuwar su cikin haɗari ta hanyar neman hanyar da ba ta dace ba don kawo ƙarshen ciki. A matsayi na na wanda ke son kare ƴan'cin mata da daidaiton jinsi, na so in binciko illar laifin zubar da ciki a Najeriya. Don haka na nemo matan da suka sadaukar da rayukan su don su kawo ƙarshen ciki. Bayan na yi magana da Seyi da Amina da Dr Annie, Ina son ƙarin sani game da yanayin doka na zubar da ciki a nan Najeriya. Don haka na nemi Timothy ɗalibin shari’a kuma lauya mai jiran gado a kan abin da yake tunani game da batun zubar da ciki.
Wannan shi ne ra'ayin sa game da zubar da ciki.
Dokar zubar da ciki a Najeriya na ƙunshe ne a cikin babban matsayi na na hukunci guda biyu. Waɗannan su ne KUNDI HUKUNTA LAIFUKA, sashe na 232 da DOKAR LAIFUKA, sashe na 228.
Ya kamata a lura da cewa yayin da dokar hukunta laifuka ta bayyana ƙarara cewa an yarda a zubar da ciki 'domin ceto rayuwar mace' dokar laifuka ta yi shiru a kan lokacin da zubar da ciki ya halatta. Amma akwai hukuncin da kotun ta yanke wanda ke nuni da hakan. Daga cikin abin da aka rubuta, illa kawai a Najeriya shi ne idan irin wannan aikin zubar da ciki ya kasance don ceton rayuwar mace. An bayyana wannan a fili a cikin kundin hukunta laifuka, amma an yi la'akari da shi daga ƙa'idodin aikata laifuka kuma tare da taimakon shari'a.
A kowane hali, ceton rai shi ne kawai hujjar doka don zubar da ciki a ƙarƙashin dokar laifuka ta Najeriya. Ma’ana, wannan ita ce kaɗai hanya ko hujjar zubar da ciki a Najeriya.
Dokar ta ƙasa ta gaza ta bayyana a fili ta haɗa bada misali da in mace ta samu ciki ta hanyar munanan ayyuka kamar fyaɗe. Misali, lamarin ƴan matan Chibok [1]. Domin baya ga akwai haɗari ga rayuwar su saboda suna ƙanana, yanayin tunanin su ma yana iya shafar su. Dokar ba ta yi hasashen waɗannan abubuwan ba.
Zubar da ciki haramun ne amma ba za a iya magance shi gaba-ɗaya ba. Hakan dai ya ƙara jefa rayuwar jama’a cikin haɗari domin a maimakon samun ƙwararrun ƙwaƙƙwaran doka, za su iya kai wa ga taimakon kan su da ƙwazo ko sarrafa abubuwa masu lahani da za su lalata lafiyar su.
A shekarar 2019 an yi hasashen adadin mace-macen mata da cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya zai kai 814 daga cikin 100000 da aka haifa. Wannan ya sa Najeriya ta zama ƙasa mafi yawan mace-macen mata masu juna biyu a duniya. Mafi muni kuma, ana samu ne sakamakon zubar da ciki ta hanyar da bata dace ba sun kai kusan kashi 40 na mace-macen mata masu juna biyu a Najeriya. Waɗannan alkalumman ƙila ma ba za a iya faɗin su ba.
Haramcin zubar da ciki yana yin illa fiye da kyau musamman idan muka yi la'akari da tattalin arziki da salon rayuwa a ƙasar. Ya kamata a bar mutane su yi yadda suke so ƙwayayen halittan, ba wai su haifi ƴayan da ba za su iya basu kulawa ba.”
[1] al’amarin da ya samu karɓywa a duniya, inda a shekarar 2014 ƴan Boko Haram suka sace ƴan mata sama da 300 daga makarantar sakandare a garin Chibok.Duk ra'ayi da fassarar shari'a na Timothy ne.
Bayanin ƙarshe
Wani abu ɗaya da ya haɗa waɗannan matan shi ne rashin maganin kafin zubar da ciki ko kuma bayan zubar da ciki. Saboda tsoron tsangwama da ɗauri, galibin matan da ke zuwa domin zubar su kan je inda zai jefa rayuwar su cikin haɗari. Waɗannan mutane kusan suna fuskantar hukunci na rashin da'a kuma suna ci gaba da amfani da lasisin su don yin illa ga mata. Ba kamar Seyi * da, Amina* da ƙaramar yarinya Dr Annie* sun yi magana game da, dubban mata sun rasa rayukan su saboda rashin tsaron hanyoyin zubar da ciki. Da fatan gwamnati za ta gane cewa zubar da ciki na kiwon lafiya ne kuma a ƙarshe ta dakatar da aikata laifuka.
*An canza sunaye masu alamar tauraro don kare sunayen waɗanda suka yi magana da Correspondents of the World bisa sharaɗin sakaye sunan su.
How does this story make you feel?
Follow-up
Do you have any questions after reading this story? Do you want to follow-up on what you've just read? Get in touch with our team to learn more! Send an email to [email protected].
Talk about this Story
Please enable cookies to view the comments powered by Disqus.
Subscribe to our Monthly Newsletter
Stay up to date with new stories on Correspondents of the World by subscribing to our monthly newsletter:
Other Stories in Hausa
Explore other Topics
Get involved
At Correspondents of the World, we want to contribute to a better understanding of one another in a world that seems to get smaller by the day - but somehow neglects to bring people closer together as well. We think that one of the most frequent reasons for misunderstanding and unnecessarily heated debates is that we don't really understand how each of us is affected differently by global issues.
Our aim is to change that with every personal story we share.
Community Worldwide
Correspondents of the World is not just this website, but also a great community of people from all over the world. While face-to-face meetings are difficult at the moment, our Facebook Community Group is THE place to be to meet other people invested in Correspondents of the World. We are currently running a series of online-tea talks to get to know each other better.